Jiragen British Airways sun koma aiki a Masar
July 26, 2019Talla
Yayin da kamfanin ke sanar cigaba da komawa jigilarsa a kasar ta Masar, ya ce tsaron lafiyar fasinjoji da ta ma'aikatan jiragen shi ne babban abin da ya sanya a gaba.
A ranar Asabar din da ta gabata ce kamfanin ya sanar da jingine dauka da sauke fasinja a babban birnin kasar ta Masar duk kuwa da cewar kawo yanzu masu ruwa da tsaki a kamfanin basu bayyana dalilan tsaron da suka haifar da wannan takaitaccen tsaiko ba, shima kamfanin jiragen sama na Lufthansa mallkar kasar Jamus ya dakatar da zuwa babban birnin na Masar amma na kwana guda, al'amarin da mahukuntan kasar Masar suka soka da kakkakusar murya.