1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bude tattaunawar Siriya da 'yan tawaye

January 23, 2017

Tawagar wakillan gwamnatin Siriya da na 'yan tawaye na soma zaman tattaunawa na gaba da gaba a birnin Astana na Kazastan.

https://p.dw.com/p/2WEVn
Genf Syrien Konferenz HNC Vertreter Opposition Mistura
Hoto: Reuters/D. Balibouse

A wannan Litinin ce ake bude zaman farko na tattaunawar keke da keke tsakanin wakillan gwamnatin Siriya da na 'yan tawayen kasar a birnin Astana wanda ke zama irinsa na farko tun bayan soma yakin kasar ta Siriya. Tawagogin bangarorin biyu sun isa tun a ranar Lahadi a babban birnin kasar ta Kazastan. 

Tawagar 'yan tawayen masu samun goyon bayan Turkiyya da kuma ta gwamnatin Siriyar mai samun goyon bayan Rasha da Iran sun bayyana bukatar ganin tattaunawar ta fara da mayar da hankali kan batun karfafa yarjejeniyar tsagaita wutar da ta fara aiki tun a ranar 30 ga watan Disamba da kuma ke tangadi a sakamakon ketata da bangarorin ke yi lokaci zuwa lokaci. 

Gwamnatin Siriyar dai na son a lokacin wannan zama a shawo kan 'yan tawayen kasar kan su mika makamansu a yi musu afuwa. Taron na birnin Astana na zama na share fage ga wanda bangarorin biyu za su yi a karkashin jagorancin Majalisar Dinkinuniya a ranar takwas ga watan Fabrairu mai zuwa.