1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na sake tsunduma cikin bashi

September 23, 2021

A yayin da ake ci gaba da korafi kan ta'azzarar cin bashi a bangaren gwamnatin Tarayyar Najeriya, kasar ta ce tana shirin dorawa tare da cin wani bashin da ya tasamma Naira zambur kusan biyar a badi.

https://p.dw.com/p/40lR8
Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Ya zuwa yanzun dai a duk wata Naira guda da ta shiga aljihun mahukuntan Najeriyar,  Kobo 67 na tafiya ne wajen biyan ruwa na bashin kasar da ke ta karuwa. An dai kiyasta cewa ya zuwa karshe na shekarar bana yawan bashin kasar zai kai kusan  Naira zambur 35, a wani abu da ke dada nuna alamun komawa rikicin bashin da ya tayar da hankali cikin kasar can baya. To sai dai kuma Abujar na shirin dorawa, tare da wani sabon bashin da gwamnatin kasar ta ce tana shirin ta ciwo domin kasafin kudi na shekarar badi.

Karin Bayani: Najeriya ta talauce dole ne a ciwo bashi

Majalisar dattawa ta kasar da ta amince da wani tsarin kisan kudi na shekarar badi ce dai, ta bai wa gwamnatin kasar izinin cin bashin da ya kai Naira zambur kusan biyar. Abujar dai na fatan amfani da kudin da nufin kammala muhimman ayyuka, kamar layin dogon da ta fara a sassa dabam-dabam cikin Najeriyar. Kuma a fadar Sanata Yahaya Abdullahi da ke zaman shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan, sun gamsu da tsarin gwamnatin da ya kai ta ga ciwo sabon bashin.

Nigeria Symbolbild Korruption
Darajar kudin Najeriya na karyewa, kana farashin kayan masarufi na kara hauhawaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Sabon bashin da ke zuwa a daidai lokacin tashin farashin man fetur na kasar dai, na janyo damuwa kan aniyar mahukuntan na aiwatar da muhimman ayyuka ba tare da bashin ba. Ko bayan man dai shi kansa tattalin arzikin kasar ya fara nuna alamun tashi daga suma, bayan da aka samu ci-gaban da ya kai na kusan kaso  biyar cikin 100 a karon farko cikin tsawon lokaci. To sai dai kuma a fadar Abubakar Ali da ke sharhi kan tattalin arzikin Najeriyar, albarkar man ta sauya daga arziki na takama cikin kasar ya zuwa rikicin da ke zaman kadangaren bakin tulu.

Karin Bayani: Layin dogo tsakanin Najeriya da Nijar

In har man fetur yana shirin barin Najeriya cikin laka dai, daga dukkan alamu batun harajin da masu mulki na kasar suka dauki lokaci suna kau da ido na shirin zaman hanya daya tilo a tsakanin Abujar da kaucewa  bashin da ke ta tayar da hankalin 'yan mulki da ma talakawa na kasar. Kuma a fadar Sanata Adamu Aleiro da ke zaman dan majalisar dattawa daga Kebbi, mayar da hankalin gwamnati kan manyan kamfanonin kasar na iya kai wa ga ninka yawan kudin shiga na Abujar a lokaci kankani. Tarayyar Najeriyar dai na tsakanin sake more rayuwa da ababe na zamani cikin halin babu, ko kuma matsar dutse da nufin samar da ruwan da ke iya kai wa ga kashe kishi a zamani na bukatun zamani.