MDD ta ce ana neman taimako gaggawa
December 2, 2021Hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta ce bukatar bada agajin gagawa ta yi karuwar da ba a taba ganin irinta ba, a sabili da annobar da duniya ke fuskanta a yanzu haka da ma matsalar sauyin yanayi da kuma tashe-tashen hankula a wasu kasashen da ke kara raba mutane da matsugunansu.
Hukumar ta OCHA ta ce akalla an yi kiyasin mutane miliyan 274 ne za su bukaci taimakon gagawa a shekarar da ke tafe. Wato karin kashi 17 cikin dari na mutanen da ake da su a yanzu haka, a cewar babban jami'in hukumar agajin.
A duk shekara sama da dalar Amirka biliyan 35 ake kashewa a kan masu bukatar agaji, sai dai saboda karin da hukumar ta ce za a samu, shekarar 2022 sai an bukaci sama da biliyan 40 idan aka yi la'akari da halin matsin da al'umma ke ciki a kasashen Habasha da Afghanistan da Myanmar da sauran wasu da dama.
A shekarar da ta gabata sama da mutum miliyan dari ne hukumar agaji ta OCHA ta kai wa dauki.