1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kisan fursunonin siyasa a kasar Iran

Binta Aliyu Zurmi
January 27, 2022

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a gudanar da binciken kisan gillar da aka yi wa dubban fursunonin siyasa a kasar Iran a shekarar 1988.

https://p.dw.com/p/46BlB
Russland Moskau, Besuch Iran Ebrahim Raisi
Hoto: Pavel Bednyakov/Kremlin/Zuma/picture alliance

Fitattun tsofaffin alkalai da masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci shugabar hukumar kare hakkin bil Adama ta majalisar Michelle Bachelet, da ta gudanar da bincike a kan kisan gillar da aka yi wa wasu fursunonin siyasar Iran a shekarar 1988, da ma irin rawar da ake zargin shugaba Ebrahim Raisi ya taka a wancan lokacin.

Wajen mutane 460 suka rattaba hannu a wata budaddiyyar wasikar da aka fidda a yau, ciki kuwa har da tsohon shugaban kotun hukunta manyan laifukan yaki watau ICC Sang-Hyun Song.

Shugaba Raisi da ke shugabantar Iran tun daga watan Augustan shekarar da ta gabata na karkashin takunkumin Amirka kan zarge zargen wasu batutuwa ciki har da kasancewa daya daga cikin alkalai 4 da suka ga kisan na shekara ta 1988.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta amnesty international ta ce mutane da ake zargin an yiwa kisan kiyashi a wancan lokacin sun kai dubu biyar ko fiye da hakan.