Bukatar kai kayan agaji Aleppo
August 27, 2016
Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Siriya Staffan de Mistura ya bukaci bangarorin da ke rikici da juna a Aleppo da su amince kan a kai kayan agaji ga wanda suke bukata daga yanzu zuwa gobe Lahadi. De Mistura ya ce dole ne kayan agajin da ake da aniyar kaiwa su bi ta babbar hanyar nan ta Castello don haka ya na da kyau bangarorin biyu su bada hadin kai wajen ganin wannan yunkuri ya kai ga tabbata.
To sai dai masu adawa da gwamnatin Bashar al-Assad wanda ke fafutuka wajen karbe iko da Aleppo din na adawa da amfani da wannan hanya wajen kai kayan agajin da kuma gyara na wutar lantarki da ruwan sha wanda jama'a ke matukar bukata. A daura da wannan, Rasha da ke dasawa da gwamnatin Assad ta ce za ta yi bakin kokarinta wajen ganin dakarun gwamnati sun bada hadin kai don a samu sukunin shiga Aleppo din yayin da Amirka da sauran kasashe ke kokarin lallabar sauran bangarorin da su ma su bada hadin kai.