1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kasar Rasha da Ukraine

Binta Aliyu Zurmi
April 10, 2022

Fafaroma Francis ya bukaci kawo karshen yakin Rasha da Ukraine da ke ci gaba da lakume rayukan mutane da ma raba wasu da dama da matsugunansu, albarkacin bikin Easter da ke tafe.

https://p.dw.com/p/49k1I
Vatikan | Papst Franziskus veruteilt das Massaker von Butscha
Hoto: AFP

Shugaban darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis ya yi kira ga kasashen Rasha da Ukraine da su tsagaita wuta albarkacin bikin Easter da ke tafe.

A jawabin da ya yi a yau Lahadi, Fafaroma ya bukaci bangarorin da ke kai ruwa rana da su mutunta wannan lokaci su maida wukaken su kube don kawo karshen yakin baki daya.

Wannan jawabi dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke kokarin kara taimaka wa Ukraine da manyan makamai da za ta kare kanta a yayin da Rasha ke zafafa kai hari a gabashin kasar.

Ko a wannan rana ta Lahadi an kai wani hari a filin jirgin sama da ke garin Dnipro da ke gabashin kasar baya ga na jirgin kasa da aka kai a Juma'ar da ta gabata wanda ya hallaka sama da mutane 50.