1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar sabon maganin Malaria a Afirka

Abdullahi Tanko Bala
April 21, 2023

Kasashen Afirka za su sayi sabon maganin maganin zazzabin cizon sauro R21 guda miliyan 20 don yaki da cutar da ta addabi al'umma a nahiyar

https://p.dw.com/p/4QQgY
World Mosquito Program | WMP staff at the insectary in Vanuatu
Hoto: World Mosquito Program

Kasashen Afirka na ci gaba da nuna bukatar amincewa da sabon maganin allurar zazzabin cizon sauro na Malaria inda aka tanadi sayar musu maganin guda miliyan ashirin a bana a cewar kamfanin da ya samar da maganin.

Hukumar kula da ingancin magunguna ta Najeriya ta bi sahun Ghana inda kasashen biyu suka zama na farko a duniya da suka amince da sabon maganin R21 wanda masana kimiyya a Jami'ar Oxford suka gano sannan kamfanin sarrafa magunguna na India tare da Novavax suka samar.

Matakin dai na zama wanda ba a saba gani ba saboda an dauke shi tun kafin hukumar lafiya ta duniya ta bada sahalewarta a kai.