Bukatar shata yankin da babu fada a Siriya
May 4, 2017Talla
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yace shirin shata wasu yankuna da za'a hana fada a cikinsu a Siriya wanda ya sami goyon bayan Rasha zai taimaka matuka wajen kawo karshen yakin basasar da aka shafe shekaru shida ana yi a kasar.
Erdogan wanda ya tattauna shirin da shugaban Rasha Vladimir Putin a ranar Laraba ya baiyana fatan cewa idan aka aiwatar da shirin zai rage da kimanin rabi yawan fadan da ke wakana a kasar ta Siriya.
Turkiyya da Rasha dai sun sha samun sabanin ra'ayi a kan yadda za'a shawo kan rikicin inda Moscow ke goyon bayan shugaba Bashar Al Assad yayin da Ankara ke kokarin ganin ya sauka daga karagar mulki.