1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kawo gyara a bangaren shari'a

Salissou Boukari LMJ
June 9, 2020

Babbar cibiyar lauyoyi ta kasa a Jamhuriyar Nijar ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce ta gano manyan matsaloli kan yadda bangaran gwamnati ke shiga sharo ba shan a cikin harkokin shari'a.

https://p.dw.com/p/3dVsY
Demokratische Republik Kongo Kinshasa | Nigerianischer Präsidenten Mahamadou Issoufou
Shugaba Issoufou Mahamadou na Jamhuriyar NijarHoto: Presidence RDC/G. Kusema

A wani taron manema labarai da lauyoyin suka yi, sun yi kira ga shugaban Jamhuriyar ta Nijar Issoufou Mahamadou da ya tabbatar da 'yncin da bangaren shari'ar ke da shi, a cearsu shine tushe na zaman lafiya da ci-gaban kasa.

Takun saka a fannin shari'a

Kafin dai wannan sanarwa, cibiyar lauyoyin ta Nijar ta ce ta lura a 'yan kwanakin nan ana samun takun saka tsakanin kungiyar alkalai ta kasa da ministan shari'a, lamarin da ya tilasta musu daukar matakin sauraron kowane bangare.
Lauyoyin sun sanar da cewa sun gano lalle gwamnati na yin katsalandan da shiga shagulan harkokin shari'ar. A cewarsu wannan lamarin na matsayin wata babbar barazana ga 'yancin zartas da shari'a a Nijar din.

Revisionsgericht in Niger
Kotun daukaka kara ta YamaiHoto: DW/M. Kanta

Kira ga masu ruwa da tsaki

Babbar cibiyar lauyoyin ta Nijar dai, ta yi kira ga shugaban kasa Issoufou Mahamadou wanda shi ne babban alkali na kasa da kuma nauyin kare kundin tsarin mulkin kasar ya rataya a kans, daa ya ya yi amfani da matsayin da kasa ta ba shi wajen gyara harkokin shari'a a kasar, tare da kaucewa daukar matakai da suka sabawa dokoki kan harkokin shari'ar.

Sun kuma yi kira ga alkalai da cewa, ganin yadda doka ta ba su izinin zartas da shari'a kuma daidai da yadda suka ga ya dace cikin tsarin doka, ya kyautu suma su bi dokar yadda shari'a za ta tsaya da kafafunta a kasar.