Bukin juyin-juya-hali a Iran
February 11, 2011A ƙasar Iran an gudanar da taruka a dangane da bukin cika shekaru 32 na juyin-juya-halin da ya tuntsurar da Sarki shah daga karagar mulki. A cikin jawabin da ya yi a dangane da wannan rana Shugaba Mahmoud Ahamadinejad ya gargaɗi masu zanga-zanga a Masar da sulura da take-taken Amirka. Ahmadinajad ya ce nan ba da daɗewa ba Masar za ta yi hannu riga da Amirka da Israila.
Jama'a da daman gaske ne dai suka yi turuwa a dandalin Azari da ke birnin Tehran da sauran biranen ƙasar bayan da 'yan adawa suka ce an kama shugabanni da magoya bayansu guda goma. An dai murƙushe 'yan adawar da suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da sake zaɓar Shugaba Ahmadinejad a shekarar 2009 . Yan adawar sun ce sai da ma a ka hana su gudanar da taro a ranar Litinin domin nuna goyon baya ga boren da ake gudanarwa a ƙasashen Larabawa.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu