Bulgeriya ta kori jami'an Rasha
March 18, 2022Talla
Matakin na zuwa ne bayan da ma'aikatar harkokin wajen kasar Bulgeriya ta kori jami'an diflomasiyyar kasar Rasha biyu a farkon watan Maris na shekarar 2022 saboda zargin aikata laifukan leken asiri.
Kungiyar tarayyar Turai da kungiyar tsaro ta NATO na da alakar tattalin arziki mai karfi da gwamnatin Rasha, amma wasu da ake zargi da laifin leken asiri sun bata dangantakar tun watan Oktoban 2019.
Sallamar jami'an Rasaha na baya-bayan nan da kasar Bulgeriya ta yi na zuwa ne a dai-dai lokacin da dangantaka tsakanin kasashen yamma da Moscow ta sake daukar sabon salo dangane da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, wanda ya haifar da takunkumin da ba a taba ganin irinsa ba, da kuma ganin Moscow ta zama saniyar ware a fannin diflomasiyya.