Lafiya
Equatorial Guinea na fama da Marburg
February 14, 2023Talla
Wakilin hukumar a Equatorial Guinea George Ameh ne ya tabbatar da matakin na WHO, inda ya ce suna bincike domin gano mutanen da suka yi hula da wadanda suka kamu da cutar ta hanyar dawo da ma'aikatan da suka gudanar da bincike kan kwayar cutar COVID-19 domin su taimaka. Tuni dai 'yar karamar kasar da ke yankin tsakiyar Afirka, ta sanar da mutuwar mutane tara daga kwayar cutar da kuma wasu 16 da ake kyautata zaton sun kamu da ita. Equatorial Guinea ta kumamma killace mutane sama da 200, tare da takaita zirga-zirga a gundumar Kie-Ntem da cutar ta fara bulla.