Bundesliga: Taurarin Afirka 10 da za a kalla a kakar wasa ta 2022/23
Daga Sadio Mane zuwa Ramy Bensebaini zuwa Amadou Haidara, yayin da ake fara gasar Bundesliga ta 2022/23, DW ta yi nazari kan manyan 'yan wasan Afirka guda goma da za su fi daukar hankali.
Sadio Mane (Senegal/Bayern Munich)
Wani yunkuri ne da ba a taba yin irinsa ba wanda ya kawo daya daga cikin manyan ‘yan wasan kwallon kafar Afirka zuwa gasar Bundesliga. Bayan nasarar shekaru shida a Liverpool, dan wasan Senegal ya koma Bayern Munich, inda ake sa ran akalla zai cike gurbin da Robert Lewandowski ya bari. Duk idanu za su kasance a kansa lokacin da Bayern ta fara kakar a wasan farko tsakaninsu da Eintracht Frankfurt.
Eric Maxim Choupo-Moting (Kamaru/Bayern Munich)
Sunan tauraro a kasarsa ta Kamaru bayan ya taimaka wa Indomitable Lions don samun gurbi a gasar cin kofin duniya ta 2022, Eric Maxim Choupo-Moting yana jin dadin matsayin da ba shi kima a Bayern Munich. Bayan tafiyar Robert Lewandowski, duk da haka, Choupo-Moting shi ne kawai babban dan wasan gaba a kungiyar, kuma zai iya zama mai amfani ga koci Julian Nagelsmann.
Ramy Bensebaini (Aljeriya/Borussia Monchengladbach)
Daya daga cikin 'yan wasan baya na hagu a Bundesliga, Ramy Bensebaini na Borussia Mönchengladbach shi ma yana da hazaka wajen zura kwallo a raga. Dan wasan mai asali daga kasar Aljeriya ya bayyana kansa da kwallaye biyu a ragar Bayern Munich a kakar wasa ta farko, kuma ya zura kwallaye 19 gaba daya a duk gasanni. Ya yi fama da rauni a kafarsa a kakar wasan bara.
Daniel-Kofi Kyereh (Ghana/SC Freiburg)
Tauraron dan kwallon Ghana Daniel-Kofi Kyereh ya shiga gasar Bundesliga bayan ya taka rawar gani tare da St. Pauli a gasar Bundesliga 2, inda ya zura kwallaye 22 a wasanni 67 da kungiyar ta Hamburg ta buga, ya kuma taimaka aka ci 21. Yayin da gasar cin kofin duniya ke tafe a watan Nuwamba, magoya bayan Ghana za su yi fatan zai iya yin irin wannan salon a Bundesliga, da kuma Black Stars a Qatar.
Sebastien Haller (Ivory Coast/Dortmund)
Sebastien Haller ya fara buga wa Borussia Dortmund a wani yanayi maras kyau wanda kuma ba ruwansa da kwallon kafa. An gano dan wasan na kasar Ivory Coast yana da cutar daji da ta shafi mazakuta kuma ana shirin yi masa magani. Har sai mun sami labari masu dadi, amma yanzu aza ayar tambaya ko dan shekaru 28 na iya zama wanda zai maye gurbin Erling Haaland ko a'a, ba su da muhimmanci.
Amadou Haidara (Mali/RB Leipzig)
Mai karanta wasan cikin basira, Amadou Haidara na Mali daya daga cikin jaruman RB Leipzig da ba a jinjinawa ba a kakar bara, yayin da suka samu nasarar lashe babban kofi na farko, wato kofin Jamus. Duk da sha'awarsa da Manchester United ta yi, mai shekaru 24 a maimakon haka ya rattaba hannu a Leipzig har zuwa 2025, yayin da kungiyar Red Bull ke kokarin kalubalantar Bayern Munich a bana
Ihlas Bebou (Togo/1899 Hoffenheim)
Daya daga cikin 'yan wasa mafi sauri a gasar Bundesliga, dan wasan Togo Ihlas Bebou ya ci wa Hoffenheim kwallaye bakwai a kakar da ta wuce - amma shirye-shiryensa na kakar wasa ta 2022/23 ya fuskanci matsala a gwiwa. Sabon kocin Hoffenheim Andre Breitenreiter, wanda ya yi aiki tare da Bebou a Hannover a baya, zai yi fatan dan wasan nasa ya kasance cikin koshin lafiya.
Ellyes Skhiri (Tunisiya/Cologne)
Mai kuzari da aiki tukuru, Ellyes Skhiri yana ɗaya daga cikin manyan 'yan wasan Bundesliga idan ana maganar tazarar kilomita a filin wasa. Kuma kocin Cologne Steffen Baumgart, yana yaba irin salon wasansa. Shi ne injiniyan tsakiya a kakar wasan da ta gabata yayin da Cologne ta yi nasarar shiga gasar UEFA - amma ko Skhiri da kungiyar da ake wa lakabi da Billy Goats za su iya zarcewa a bana?
Chidera Ejuke (Najeriya/Hertha BSC)
Wanda ya yi suna wajen iya murza leda, Chidera "Chiddi" Ejuke ya zama wanda aka fi so tare da CSKA Moscow Premier League na Rasha. A wannan kakar, ya koma Hertha Berlin a matsayin aro, inda zai taka leda a karkashin fuskar da ya sani daga Moscow, babban koci Sandro Schwarz, wanda kwanan nan ya jagoranci Dynamo Moscow. Hertha za ta yi fatan Ejuke zai iya taimaka mata kauracewa fita daga Bundesliga.
Omar Marmoush (Masar/VfL Wolfsburg)
Bayan wasanni biyu a jere yana zaman aro a St. Pauli da VfB Stuttgart, wannan na iya kasancewa kakar da dan wasan gaba na Masar Omar Marmoush ya haskaka a gasar Bundesliga tare da VfL Wolfsburg. Dan wasan mai shekaru 23 ya riga ya zama babban dan wasa ga 'yan tawagar ta Fir'auna a matakin kasa da kasa, yanzu ne lokacin da za a nemi gurbi a kungiyar Wolfsburg ta Niko Kovac.