Ingantuwara cinikin albasa a Jamhuriyar Nijar
February 7, 2024Mataki na gaba dai bayan saka wannan hannu tsakanin kamfanonin kasashen biyu, shi ne na samar wa kamfanin SOTRACO na kasar Nijar kayayaki masu inganci na zamani da za su bada damar noma isassar albasa da kuma sarrafata ta yadda manoma za su rinka samun kudadan shiga da samar da guraben ayyukan yi masu yawa. Kuma a cewar Ali Samba Diabri Magatakardan ofishin ministan kasuwanci na Jamhuriyar Nijar wannan wata dama ce ta karfafa hulda da Togo da ke a matsayin babbar kawa ta kasar Nijar a wannan lokaci.
Karin Bayani: Nijar: Takaddama kan amfani da kudin CFA
Kamfanin na kasar Togo na CALAFI Agro da ya shahara kan inganta harkokin noma da sarrafa kayayakin da ake nomawa, kuma da yake magana babban Darecta Janar na wannan kamfanin Lambert Nayante ya ce lalle ne kamfaninsu ya shahara a fannin bayar da horo da kuma samar da ingantattun kayayakin noma na zamani.
Wannan kamfani dai mai kula da sarrafa albasa na kasar Nijar ta bakin shugabansa Alhaji moustapha Kadri sarkin Abzin, sun sashe kimanin shekaru 20 su na kokowar ganin sun samu budi da cikeken tallafi daga magabata don ganin albasar da ake nomawa a Jamhuriyar Nijar ba ta ci gaba da rubewa ba. Wannan yarjejeniya ta kasashen biyu bayan ma karfafa hulda ta dangantaka burin da ta sa wa gaba shi ne na bunkasa fannin albasa ta hanyar samar da masana'antu da sarrafa albasa da nomanta a kan fadin kadada kusan 50,000 domin samar da albasa mai yawa da kuma inganci.