Mayaka sun halaka sojojin Burkina Faso
May 19, 2022Talla
Rundunar sojojin kasar ta Burkina Faso ta ce hari na biyu ya halaka farar hula daya, tare da jikkata wasu da dama da ke cikin motar fasinja. Harin ya faru ne bayan wani makamancinsa da ya kashe kusan mutane 40 a ranar Asabar din da ta gaabata. Yawancin wadanda harin ya rutsa da su dai, fararen hula ne masu aikin sa kai tare da sojoji.
Burkina Faso dai ta sha fama da hare-haren masu jihadi tun shekara ta 2015, tare da yunkurin da ke da alaka da Al-Qa'eda da kungiyar IS. Sama da mutane 2,000 ne aka kashe, yayin da wasu miliyan daya da dubu 800 suka rasa muhallansu. Sabon shugaban kasar Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba dai, ya yi alkawwarin bai wa matsalar tsaro fifiko.