1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin kifar da gwamnati ya ci tura a Burkina

Abdourahamane Hassane
September 8, 2023

Hukumomim shari'a a Burkina Faso sun ce an cafke wasu sojojin guda uku wadanda suka yi kokarin kitsa makirci wa gwamnatin mulkin sojin kasar.

https://p.dw.com/p/4W8Nf
Burkina Faso | Soldaten in Ouagadoudou
Hoto: Kilaye Bationo/AP Photo/picture alliance

Alkali soji mai shigar na kasarya ce ana tuhumar sojojin guda uku da yin zagon kasa wa tsaron kasa. Sojojin wadanda dukkaninsu suka amince da tuhumar kan cewar sun yi yunkuri neman kiffar da gwamnatin mulkin sojinmai ci yanzu ta kaptain traore . An koresu daga aikin soji tun a shekarar ta 2015.Daman a  cikin watan Disamba bara, wasu sojoji da farar hula a karkashin jagorancin, Laftanar-Kanar Emmanuel Zoungrana,sun so yin juyin, sai dai ba su yi nasara ba kuma yanzu suna daure a gidan yari.