Burkina Faso: An kashe mutane 170 cikin mako guda
March 3, 2024Talla
Dan sanda mai gabatar da kara na Burkina Faso, Aly Benjamin Coulibaly ya ce, sun samu rahotannin kai hare-hare a kauyukan da ke lardin Yatenga a ranar 25 ga watan Fabarairun da ya gabata.
Kazalika an kai wasu mabambantan hare-hare a wani masallaci da kuma mujami'a da ke arewacin kasar.
Tuni dai aka kaddamar da bincike kan harin da ya raunata gomman mutane da kuma lalata dukiyoyi. Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.
Kasar Burkina Faso ta sha fama da rikcin kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai da suke da alaka da Al-Qaeda da kuma IS.