AU ta yi tir da tsare Shugaba Kabore
January 24, 2022Talla
A wata sanarwa da Shugaban kungiyar AU Moussa Faki Mahamat ya fitar, ya yi kira ga sojojin Burkina Faso da jami'an tsaro, su tabbatar da
hakkinsu na tsaron kasa tare da kare lafiyar Shugaba Kabore da mambobin gwamnatinsa da suka kama.
Sojojin Burkina Faso sun sanar da tsare Shugaba Kabore da ministocinsa kwana guda bayan da 'yan tawaye suka kwace wani barikin soji, inda suka yi ta artabu da bindigogi a babban birnin kasar da ke yammacin Afirka.
Ba a dai bayyana ko wane ne ke rike da ragamar mulkin kasar ba zuwa yanzu, amma wata sanarwa a shafin Twitter na Shugaba Roch Marc Christian Kabore, ya yi kira ga sojoji da su ajiye makamansu, duk da cewa sojoji sun yi kawanya a kafar yada labaran kasar.