1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso na kokarin warware babbar rigima

Abdoulaye Mamane Amadou M. Ahiwa
July 7, 2022

Gwamnatin soja ta wucin gadi a Burkina Faso ta tabbatar da komawar hambararren shugaban kasar Blaise Compaoré a kokari na sasanta rikicin siyasa mai nasaba da tsaro.

https://p.dw.com/p/4Do8Q
Blaise Compaoré Präsident Burkina Faso
Hambarerren shugaban kasar Burkina Faso, Blaise Compaoré Hoto: AP

Guguwar siyasar da ta barke bayan mummunan zanga-zanga da ta kori hambararren shugaban kasar Blaise Compaoré bayan shafe shekaru fiye da 20 yana jan zarensa kan karagar mulki.

Sai dai tun bayan ficewar tasa inda ya samu mafakar siyasa a matakin farko kafin a ba shi takardar shaidar zama dan kasa, Compaoré ya makale ne a Cote d'ivoire, inda daga can yake kallon halin da kasar ta fantsama tun bayan barkewar boren, kafin matsalar tsaro ta yi wa kasar kamun kazar kuku.

Neman mafita kan matsalolin da ke addabar kasar da sulhunta rikicin siyasa, su suka tilasta wa gwamnatin wucin gadin kasar neman yin tozali da hambararren shugaban kasar Blaise Compaoré. Tun daga kasar da yake gudun hijira bayan hambarar da shi a 2014, shugaban ya aminta da ya tattauna da gwamnatin a wannan Jumma'a a cewar Amadou Coulibaly kakakin gwamnati.

Sai dai masana kimiyar siyasa a kasashen yankin Sahel irin su Dr. Dicko Abdourahmane na jami'ar Damagaram, na ganin cewa duk wani komawar da Balaise Compaore zai yi a gida ba zai tsinana komai kan matsalolin da kasar ta ke fuskanta ba.

Thomas Sankara ARCHIV
Tsohon shugaban kasar Burkina Faso, Thomas SankaraHoto: Getty Images/AFP/A. Joe

A cikin watan Afrilun da ya gabata ne dai wata kotun koli ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga tsohon shugaban, bayan da ta same shi da aikata laifin kisan jama'a da musamman ma Thomas Sankara da ya yi wa juyin mulki a shekarar 1987, abin da ke sanya ayar tambaya kan hujjojin da suka kai sojan kasar gayyatar shi zuwa gida alhali kuwa yana karkakshin hukuncin kotu.

Idan har ba a yi wa Shugaba Blaise ahuwa ba to ba shakka dawowarsa ka iya yin fito na fito da hukuncin shari'a duba da yadda ake ganin hakan ka iya taka hakkin shari'a. Manazarta harkokin siyasa irin su Dr. Dicko Abdourahmane na mai ganin cewa zartar da hukunci ne kawai ya ragewa shugaban.

Ko bayan Shugaba Blaise Compaoré akwai tsoffin shugabannin kasar ta Burkina Faso da ke shirin haduwa domin tattaunawar da suka hada da Jean-Baptiste Ouedraogo  da ya mulkin kasar a 1982 da Isaac Zida da Michel Kafando da Roch Marc Christian Kaboré, da Dani Ba, wanda ake ganin zai kasance matattakalar farko ta kawo karshen rikici.