1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fatatakar 'yan ta'adda a arewacin kasar

Binta Aliyu Zurmi
June 21, 2022

Sojoji a Burkina Faso sun bukaci al'umma kauracewa matsugunnensu, domin fatatakar 'yan ta'adda da ke gwagwarmaya da makamai.

https://p.dw.com/p/4D0xs
Burkina Faso I Flucht und Migration
Hoto: BURKINA FASO'S PRESIDENTIAL PRESS SERVICE/REUTERS

Rahotanni daga Ouagadougou babban birnin Burkin Faso na nuni da cewar dakarun sojin kasar sun umurci al'umma fararen hula da ke a wasu yankunan arewacin kasar da ma wasu yankuna a kudu maso yammacin kasar na su kauracewa gidajensu a shirye-shiryen fatatakar 'yan ta'adda da ke a yankunan.

Da yammacin jiya ne dakarun sojojin suka fidda wannan sanarwa, sai dai babu karin bayani a game da tsawon lokacin da wannan aikin zai dauka da ma inda wadannan mutanen za su je.

A yan baya-bayan nan ayyukan ta'addanci a kasar na kara karuwa, ko a tsakiyar wannan watan an kai wani mummunan hari a yankin arewacin kasar da ya hallaka fararen hula sama da 100

Tun shekarar 2015 kasar ta Burkina Faso da ke yammacin Afirka ke fama da ayyukan 'yan ta'adda da ke da alaka da kungiyar al Qaeda wanda ya zuwa yanzu dubban mutane ne suka rasa rayukansu wasu miliyoyi na gudun hijira.