1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: An hambarar da gwamnatin Damiba

September 30, 2022

Wani gungun sojoji ya sanar a gidan Talabijin na Burkina Faso cewa ya hambarar da shugaban gwamnatin mulkin soji Paul-Henri Damiba. Matakin ya biyo bayan juyin mulkin da Damiban ya jagoranta a watan Janairu.

https://p.dw.com/p/4HcCB
Kanar Paul-Henri Damiba da aka yi wa juyin mulki a Burkina Faso
Kanar Paul-Henri Damiba da aka yi wa juyin mulki a Burkina FasoHoto: BURKINA FASO'S PRESIDENTIAL PRESS SERVICE/REUTERS

Sojojin da suka kifar da dan uwansu sun sanar da sunan Kyaftin Ibrahim Traore a matsayin sabon jagoran kasar da ke a Afirka ta Yamma.

Traore ya ce ya rusa gwamnati da kundin tsarin mulkin Burkina Faso, yana mai cewa sun dauki wannan mataki domin dawo da tsaro da martabar kasarsu. 

Sanarwar na zuwa ne sa'o'i bayan da aka ji karar harbe-harbe a kusa da babban barikin soji da ke cikin shelkwatar kasar, Ouagadougou.