Yan bindiga sun kashe mutum 10
November 2, 2021Talla
A yayin da al'umma a Burkina Faso ke tsakiyar jimamin kisan wasu jami'an 'yan sanda da 'yan bindiga suka halaka a karshen mako, wasu mahara sun sake kai wani sabon hari da yayi sanadiyar rayukan fararen hula goma. Yan bindigan sun afkawa mutanen ne, a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwan yankin da ke a arewacin kasar.
Hare-haren na ranakun Lahadi da Litinin, na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke bikin cika shekaru sittin da daya da kafa rundunar sojin kasar. Shugaba Roch Kabore a yayin jawabinsa ga manema labarai, ya ce, kasar ba za ta yi kasa a gwiwa ba duk da wadannan kalubale, a maimakon hakan ma, za ta kara zage damtse a yakin da take yi da ta'addanci.