1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa da Burkina ana tsamin dangantaka

Abdoulaye Mamane Amadou
January 22, 2023

A daidai lokacin da matsalar tsaro ke kara ta'azzara a wasu sassan kasar, gwamnatin Burkina Faso ta umarci dakarun Faransa da su fita daga kasar na da wata guda.

https://p.dw.com/p/4MY1q
Burkina Faso | Französische Armee
Hoto: Michele Cattani/AFP/Getty Images

Kamfanin dillancin labaran Burkina Faso AIB, ya ruwaito cewa hukumomi sun bukaci da Faransa ta gaggauta janye dakarunta da ke jibge a Burkina Faso nan da wata gaya.

Wasu rahotanni sun nuna cewa a baya bayan nan an jiy shugaban gwamnatin mulkin rikon kwarya na kasar Ibrahim Traoré na shaida wa wani gungunn dalibai cewar nan da 'yan kwanaki masu zuwa za su ji wasu muhimman labarai, a kokarin da kasar ta ke da shi na kare 'yancin kanta. 

Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da hulda tsakanin Rasha da Burkina Faso ke cigaba da daukar harami.

A makon da ya gabata, Faransa ta aike da manzo na musamman a birnin Ouagadoudou don ganawa da hukumomin kasar kan batun inganta huldarsu da ta kara sukurkucewa a baya bayan nan.