1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An nada sabon shugaban gwamnati a Burkina Faso

Abdoulaye Mamane Amadou
December 11, 2021

Kwanaki bayan da shugaba Roch Kaboré ya roshe majalisar ministoci a Burkina Faso bisa matsin lambar al'umma saboda tabarbarewar tsaro an nada sabon shugaban gwamnat.

https://p.dw.com/p/447jJ
Burkina Faso Lassina Zerbo
Hoto: Joe Klamar/AFP

Mai shekaru 58 a duniya Lassina Zerbo na a matsayin wata bakuwar fuska a idon jama'a a Burkina Faso, duk da yake a baya ya rike mukamin jagoran hukumar yaki da makaman kare dangi ta Majalisar Dinkin Duniya har na tsawon shekaru.

Tun a gabanin nadinsa shugaban Burkna Faso Roch Marc Christian Kaboré ya yi kira ga 'yan kasar da suka zama tsintisya madaurinki daya dan tunkarar hare-haren 'yan ta'adda da suka yi kaka gida kasar.

Nan gaba ne dai ake sa ran sabon shugaban gwamnatin ya bayyana sunayen 'yan majalisar ministocinsa, to amma sai dai babban kalubalen da ke gabansa su ne na rage kaifin hare-haren 'yan ta'adda masu ikrarin jihadi da suka mamaye yankuna da dama na kasar.