Burkina Faso: 'Yan bindiga sun kai hari
September 27, 2022Talla
A cikin sanarwar da rundunar sojin kasar Burkina faso ta fitar a Ouagadougou babban birnin kasar, ta ce 'yan bindigan sun kai hari ne kan wata tawaga da ta samu rakiyar jami'an tsaron da ke kokarin kai kayayyaki ga mazauna yankin da ke kusa da Gaskinde a yankin Sahel. Sanarwar ta kuma ce da dama daga cikin tawagar sun jikkata, kuma tuni dai aka tura da karin dakaru yankin don kwantar da hankula da kuma kai dauki ga wadanda harin ya rutsa da su.
Kasar Burkina Faso na fuskantar hare-haren 'yan tayar da kayar baya na kungiyar Al-Qaeda, inda ko a farkon wannan watan Staumba, shugaban majalisar mulkin sojin kasar Laftanal Kanal Paul-Henri Damiba ya tsige Ministan tsaron kasar bayan wasu jerin hare-hare ta'addanci da aka kai.