1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan sanda sun fatattaki masu zanga-zanga a Burkina Faso

November 27, 2021

Jami'an tsaron dai sun farma mutanen da suka fara taruwa a dazu da safiyar Asabar din nan a birnin Ouagadougou domin ci gaba da zanga-zangar adawa da yadda tsaro ya tabarbare.

https://p.dw.com/p/43ZRT
Burkina Faso Rede Präsident Roch Marc Christian Kabore
Hoto: facebook.com/Presidence.bf

'Yan sanda a Burkina Faso sun tarwatsa masu zanga-zangar rashin tsaro a babban birnin kasar a wannan Asabar.

Tun daga kisan da aka yi wa sojoji na baya-bayan nan 'yan kasar sun gudanar da zanga-zanga daban daban. A makon da ya gabata har sai da suka huce takaicinsu kan sojojin Faransa da ke wucewa a kasar ta hanyar toshe musu hanya.

Sai dai hukumomi sun mayar da martani ta hanyar katse layukan waya tare da daukar matakai na ci gaba da tarwatsa zanga-zangar da ake zulumin ka iya yin karfi ta kawar da gwamnatin kasar. To amma MDD ta yi gargadin duk wani yunkuri na juyin mulki ta hanyar fakewa da lamarin