Ana yin Allah wadai d juyin mulkin Burkina
January 25, 2022Talla
Babban sakataran MDD Antonio Guterres, ya ce ba za su taba amincewa ba da juyin mulkin sojoji ba a yammacin Afirka wanda ya yi kira ga sojoji da su kare kasashensu daga 'yan ta'adda a maimakon kodayen kwatar mulki.Tun farko kungiyar ECOWAS da kungiyar tarayar Afirka sun yi Allah wadai da juyin mulkin. Dubban jama'a a Burkina Faso sun gudanar da gamgami na nuna goyon baya ga sojojin da suka kifar da gwamnatin farar hular.