1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare mafi muni a Burkina Faso

Abdourahamane Hassane
March 14, 2022

Gwamnatin mulkin soji ta Burkina Faso na fuskantar tashin hankalin mafi muni na masu jihadi bayan wasu hare-haren da 'yan ta'addar suka kai,  tun bayan da sojojin suka karbi mulki a cikin  watan Janairun,da ya gabata 

https://p.dw.com/p/48TTw
Symbolbild Burkina Faso  Mehr als 138 Tote bei Anschlag
Hoto: Issouf Sanogo/AFP

Fararen hula 23 da Jandarmomi 13 ne suka mutu a wasu jrerin hare-hare guda hudu a cikin 'yan kwanakin nan a yankin Dori daya daga cikin manyan garuruwan arewa maso gabashin kasar. Wannan hari shi ne mafi muni tun bayan zuwan shugaba Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba, kan mulki. A cikin watan Faibrairun da ya gabata Kanal Damiban ya hambarar da gwamnatin Shugaba Roch Marc Christian Kaboré a kan dalilan gaza magance matsalar rashin tsaro .