Burkina ta nemi Faransa ta janye jakadanta
January 4, 2023Talla
Gwamnatin mulkin soji ta Burkina Faso ta bukaci Faransa ta janye jakadanta Luc Hallade daga kasar, a daidai lokacin da kin jinin Faransa ke ci gaba da bazuwa a kasar da ke Afirka ta Yamma wacce ke kokarin kara karfin dangantaka da kasar Rasha.
Mai magana da yawun gwamnatin Burkina Faso Jean-Emmanuel Ouedraogo ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na Associated Press wannan mataki. Sai dai ya kauce wa yin karin bayani a kan lamarin.
Ofishin jakadancin Faransa da ke Ouagadougou ya ce ya samu kwafin takardar da aka aike masa da wannan bukata amma bai yi wani karin haske ba.