Burtaniya za ta turawa Ukraine makamai
January 14, 2023Firanminstan Birtaniya Rishi Sunak ya yi alkawarin turawa Ukraine motocin yaki masu sulke. Wannan dai na kasance karon farko da wata kasa a yammacin Turai da za ta turawa Kyiv manyan makamai da take ta mika bukata. Shugaba Sunak ya ce, wannan wani mataki ne na Burtaniya domin kara nuna goyon bayanta ga Ukraine. Kasashen Turai da ke kawance da Ukraine dai sun turawa Kyiv motocin yaki fiye da 300 tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamaya a kasar.
Sai dai kuma Rasha ta ce hakan ka iya rura wutar yakin kasar. Offishin jakandancin Rasha a Burtaniya ya ce, babu abun da kai manya makamai zuwa yankin da ake yaki face, kara haifar da asarar rayuka ciki har da na fararen hula.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine ya mika godiyarsa ga Burtaniya, ya na mai cewa hakan yai kara karfafa Ukraine a fagen daga.