Burundi: Al'umma na cikin mawuyacin hali
April 26, 2016Da dama daga cikin 'yan siyasar kasar da kuma jami'an kungiyoyin farar hula sun ficce daga kasar sakamakon yadda suke fuskantar gallazawa daga jami'an tsaro, baya ga irin matsaloli da halin kunci da al'umma ke ciki sakamakon rashin tallafin da kasar ke samu daga kungiyoyin bada agaji da abokan arziki.
Tuni dai al'umma suka fara kokawa game da halin da ake ciki wanda yanzu haka ya fara shafar bangaren ilimi har ma wani dalibi ya ke cewar ''tun lokacin da aka fara yin tashin hankali a kasar dalibai da yawa sun watse, wasu sun hijira a cikin wasu kasashe makobta wasu an kamasu yain da wasu kuma ma sun mutu sakamakon ukubar da aka rika gana musu kuma nan da watanni kadan ne za mu sake komawa karatun amma ga yadda abubuwan suke tafiya.''
Yanzu haka dai tattalin arzikin kasar ta Burundi ya yi kasa da maki 7.5 a shekara da ta gabata saboda halin da kasar ta ke ci abin da ya janyo talauci da fatara da kuma kara hahawar farashin kayan abinci da sauransu a kasar. Wannan ne ma ya sanya wani dan kasar da ke ganin lokaci ya yi da jama'a za su nemawa kansu mafita inda ya ke cewa ''ya kamata mutane su daina tayar da fitina domin a zauna a tattauna don a dakatar da tashin hankali.''
Rikicin da ya biyo bayan tazarcen shugaban kasar dai shi ne ummul aba'isin shiga halin da kasar ta ke ciki kuma tuni kasashen duniya musamman ma wanda ke makota da Burundi din ke fadi tashi wajen ganin an shawo kan wannan matsala domin fidda al'ummar kasar da cikin kangin da suke ciki da nufin samun yin rayuwa cikin walwala kamar sauran mutane.