Burundi: Jama'a da dama sun fito kada kuri'a
May 17, 2018Al'ummar Burundi na kada a wannan Alhamis kuri'ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda zai bai wa Shugaba Pierre Nkurunziza damar sake tsayawa takara a karo na hudu da kuma ci gaba da shugabancin kasar har zuwa shekara ta 2035.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa jama'a sun fito da dama domin kada kuri'ar tasu inda ake iya ganin dogayan layuka a gaban runfunan zaben wanda ke gudana a cikin tsauraran matakan tsaro inda aka girke jami'an tsaro cikin damara da tankokin yaki a wurare da dama.
Bayan kada kuri'arsa, Shugaba Nkurunziza wanda ya isa a rumfar zaben a cikin tufafin motsa jiki da hular Kaboyi tare da mai dakinsa, ya yi kira ga 'yan kasar da su fito su kada kuri'arsu wanda 'yanci ne da doka ta ba su.
Manyan kasashen duniya dai sun yi tir da Allah wadai da wannan zaben raba gardama da zai bai wa Shugaba Nkurunziza wanda ke kan karagar mulkin kasar ta burundi tun a shekara ta 2005 damar cigaba da yin tazarce kan shugabancin kasar.