Rahoton cin zarafin jama'a a Burundi
September 5, 2018Talla
Jami'an binciken dai sun dora laifin aikata cin zarafin jama'ar a Burundi, a kan kalaman shugaban kasar Pierre Nkurunziza da suka ce sun kasance na kiyayya da tayar da tarzoma. A rahotonsa na farko da ya fitar a shekarar da ta gabata ta 2017, kwamitin Majalisar Dinkin Duniyar mai gudanar da bincike a kan tashe-tashen hankula a Burundin ya nunar da cewa yana da dalilan da zai sa ya amince cewa gwamnati ce ke da alhakin ayyuka na cin zarafin jama'a a kasar da suka hadar da kisan ba gaira da kame mutane ba tare da wani dalili ba da azabtarwa da kuma azabtarawa ta hanyar yin lalata da mutanen.