Burundi ta kori jami'an hukumar lafiya WHO
May 14, 2020Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce jami'an suna zaman kansu ne a saboda haka ta umarcesu su hanzarta ficewa daga kasar ta gabashin Afirka zuwa rsnsr 15 ga watan Afrilu a cewar wata sanarwa da ministan harkokin wajen kasar Ezechiel Nibigira ya sanyawa hannu.
Daraktan hukumar lafiyar ta duniya mai kula da shiyyar Afirka Matshidiso Moeti ta ce suna tuntubar hukumomin na Burundi domin tantance dalilin da ya sa suka dauki wannan mataki.
A ranar 20 ga watan Mayu Burundi za ta gudanar da zaben shugaban kasa yayin da ake tsakiyar annobar corona domin zaben shugaban kasa da zai maye gurbin shugaba Pierre Nkurunziza.
Hukumar lafiyar ta duniya ta ce idan har za a gudanar da zabe a tsakiyar annoba to wajibi ne a yi hakan bisa tsauraran dokoki na matakan lafiya.