1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Bush: Kuskure ne janye dakaru daga Afghanistan

July 14, 2021

Tsohon shugaban Amirka, George W. Bush, ya bayyana matakin janye dakarun kasar da na kungiyar tsaro ta NATO daga Afghanistan a matsayin wani babban kuskure.

https://p.dw.com/p/3wTBs
Merkel zu Besuch auf George W. Bushs Ranch in Texas
Hoto: Matthew Cavanaugh/dpa/picture-alliance

 

Mr. Bush wanda a zamanin mulkinsa ne aka jibge dakarun na kasashen waje a Afghanistan, ya ce yana tausaya wa rayuwar mata da 'yan mata musamman daga ta'adin da mayakan Taliban ke iya yi musu.

A wata hira ta musamman da ya yi da babbar editar DW da ke Washington Ines Pohl, George W. Bush, ya ce wadannan mayaka marasa imani na iya kama yayyanka mutan da sauran mutanen da suka taimaka wajen durkusar da su a baya.

Ganawar da ya yi da tashar ta DW, ta dubi karshen wa'adi ne na shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, wanda ya ce yana da yakinin cewa ita ma ba ta ji dadin janye dakarun daga Afghanistan da aka yi ba.

Shekaru 20 da suka gabata ne dai Amirka ta aike da dakarun a Afghanistan bayan harin nan na ranar 11 ga watan Satumba da ya jijjiga duniya.