Bush ya kammala ziyarasa a yankin Gabas ta Tsakiya
January 11, 2008Talla
Shugaban Amurka George Bush ya kammala ziyararsa ta kwanaki uku zuwa Israila da yankin yamma da gaɓar kogin Jordan. Tun da farko Bush ya kai ziyara cibiyar tunawa da yahudawa da aka kashe a yaƙin duniya na biyu a birnin Ƙudus. Bayan ziyararsa a wannan yanki Bush ya faɗawa manema labarai cewa wannan gini tuni ga jama’a cewa dole ne a yaƙi sheɗanci a koina. A ranar Asabar Bush ya baiyana tabbacinsa cewa za a iya cimma yarjejeniyar zaman lafiya kafin ya sauka daga mulki a ƙarshen wannan shekara. Bayan kuma ganawarsa dabam dabam da shugaban Palasdinwa Mahmud Abbas da kuma firaministan Isra’ila Ehud Olmert, Bush ya yi kira ga shugabbanin biyu da su ɗauki tsauraran matakai da ake bukata don tabbatar da zaman lafiya a yankin.