1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arzikin Côte d'Ivoire ya shiga wani hali

June 16, 2020

Kasar Côte d'Ivoire ta roki kasashe da hukumomin da suke bin ta bashi su daure su ba ta damar hutawa daga ci gaba da biyan basussukan.

https://p.dw.com/p/3drSx
Elfenbeinküste | Präsident Alassane Ouattara spricht während der offiziellen Zeremonie der Verkündung der dritten Republik der Elfenbeinküste nach dem Referendum über eine neue Verfassung
Hoto: REUTERS/T. Gouegnon


Sanarwar gwamnatin kasar ta ce tana son ta yi amfani da kudin da take da su a hannunta wurin inganta asibitocin kasar don tunkarar annobar coronavirus. Kazalika idan har kasashen suka tsahirta mata biyan bashin, za ta yi amfani da dukiyar wurin bunkasa tattalin arzikin kasar wanda corona ta kassara.

Sanarwar gwamnatin ta ce tuni kasar ta Côte d'Ivoire ta tura wa kasashen da ke binta bashi wannan roko a hukumance, inda take son a daga mata kafar ci gaba da biyan bashin akalla dala milyan 205.