CDU ta dinke baraka kan raunin shugabanci
November 23, 2019Talla
A wani mataki na nuna alamun dinke barakar da ke neman kunno kai a jam'iyyar CDU ta Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel shugabannin jam'iyyar sun cimma kudurin mara baya ga jagorancin shugabar jam'iyyar Annegret Kramp-Karrenbauer
Bisa al'ada jam'iyyar CDU na fidda wanda zai mata takara ba tare da mambobinta sun yi zabe ba, sai dai a wannan karon rukunun matasa a jam'iyyar sun so a jingine tsohuwar al'adar jam'iyyar domin sake zabe don samarwa jam'iyyar sabuwar makoma.
Yayin taron jam'iyyar na shekara-shekara Annegret Kramp-Karrenbauer ta kare dukkannin tsare-tsare da manufofinta da ake suka, daga bisani taron jam'iyyar ya amince da kudurin jagorancinta.