1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

CDU ta lashe zaben North Rhein Westphalia

Zainab Mohammed Abubakar
May 14, 2017

Jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta samu gagarumin rinjaye a zaben fitacciyar jihar North Rhein Westphalia da ya gudana a wannan Lahadi.

https://p.dw.com/p/2cxSl
Deutschland Landtagswahlen in NRW Armin Laschet
Hoto: picture-alliance/dpa/O. Berg

Jam'iyyar CDU mai mulki ta lashe kujerun majalisar jihar da kashi 34.5. Zaben na yau dai na zama zakaran gwajin dafin zaben gama gari da ke tafe a watan Satumba, bisa la'akari da muhimmancin jihar ta North Rhein mai mafi yawan al'umma da karfin tattalin arziki a Jamus.

Hakan kazlika ya karawa Merkel kwarin gwiwar fafutukarta na neman zarcewa a  karo na hudu, a matsayin shugabar gwamnatin wannan kasa da ta fi ko wacce karfin tattalin arziki a Nahiyar Turai.

Nasarar CDU ya kawo karshen gwamnatin jami'iyyar SPD na Fremiya Hannelore Kraft, wadda kazalika ta yi murabus daga shugabancin jam'iyyar a wannan jiha.

Mutane miliyan 13 a cikin mazauna jihar ta North Rhine Westphalia miliyan 18 ne suka cancanci kada kuri'u, wanda ke wakiltar sama da kashi daya daga cikin biyar na yawan al'ummar kasar ta Jamus.