CDU ta Merkel ta sha kaye a Zaɓen jihar Mecklenburg-Vorpommern
September 5, 2011Jam'iyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sha kaye a zaɓen gwamna da na 'yan majalisan jiha da ya gudanar a Mecklenburg -Vorpommern da ke zama jiharta ta asali. Sakamakon wannan zaɓe da aka gudanar a ƙarshen mako ya nunar da cewar ita jam'iyar da ke riƙe da madafun ikon Jamus, ta samu koma bayan kashi 28,8% idan aka kwatanta da zaɓen shekaru biyar da suka gabata. Ita jam'iyar ta CDU ta tashi da kashi da kashi 23,2% na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da jam'iyar SPD da ta yi mata kintikau ta lashe kashi 35,6% na ƙuri'un da aka kaɗa.
Ana kyautata zaton cewar ita dai jam'iyar ta SPD da ke cikin gwamnatin Haɗaka a wannan jiha, za ta iya ƙulla ƙawance da ta jam'iyar da ta zo ta uku a zaɓen ko kuma jam'iyar da ke da rajin kare muhalli domin samun damar kafa gwamnati a wannan jiha. Jam'iyar Free Demokrat da ita ma ke cikin gwamnatin haɗaka ta Merkel ba za ta samu wakili a majalisar jihar ta Mecklenburg-vorepommern ba, sakamakon lashe kashe 2,8% na ƙuri'un da aka kaɗa. Sai dai Jam'iyar NPD da ke cikin ruƙunin masu adawa za ta sami wakilci a majalisar dokokin ta wannan jiha sakamakon samun sama da kashi biyar daga cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala