Cece ku ce akan rashin lafiyar shugaban ƙasar Aljeriya
April 30, 2013Abdelaziz Bouteflika wanda ke akan karagar mulki tun a shekarun 1999 ya harbu da wata cutar ne da ake kira da sunnan "Ischemie Transitoire Sans Sequelle." Wacce jini ke yin gudaji a cikin ƙwaƙwalwa ya hana gudawar jini a cikin jiki, abinda ke janyo tsayawar zuciya ,ko kuma mutuwar rabin jiki nan take, Inda ba a yi magani ba. To amma shi likitan shugaban ya ce bayan afkuwar lamarin shugaban ya sha babu abinda ya same shi.
Rashin lafiyar tasa dai na zuwa ne a sa'ilin da ya rage shekara guda a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a shekara baɗi, a ƙasar da ke bisa danja dangane da barazana da ta ke fuskanta ta sake ɓarkewar fafutukar masu kishin addini bayan wada aka yi fama da ita a farkon shekarun 1990.
A karon farko hukumomi sun bayyana rashin lafiyar shugaban
A tarihin siyasar Aljeriya dai ba kasafai ba ne idan shugaban ƙasa ba ya da lafiya ake sanar da al'umma a halin da ya ke a ciki. To amma a wannan jikon shugaban shi da kansa ne, ya nemi a sanar da al'ummar cewar ya na yin jinya. Sherif Freski shi ne Editan wata mujalar ta Aljeriya El Kabar.
Ya ce :'' Ofishin fira minista shi ne ke ba da labarin rashin lafiyar ta shugaban jefi jefi, akan kafofin watsa labarai, sannan kuma ya ƙara da cewar a kwai wani Profeser da ya yi magana da shugaban wanda shugaban ya ummarce shi da ya sanar da yan jarida halin da yake ciki.''
Wannan dai, ba shi ne ba karo na farko da shugaban ya kwanta a asibiti , a shekarun 2005 ya kwashe lokaci mai tsawo ya na yin jinya a Faransa. To amma a yanzu a kan wanan rashin lafiya tasa jama'a sun fara azza ayyar tambaya kan cewar ko za a yi wani zaɓen shugaban ƙasar kafin lokacin, wato shekarar baɗi, ko kuma shugaban zai sake tsayawa takara a karo na fuɗu jere a wa'adiin mulkin shekaru biyar.
Mahawara akan makomar siyasar ƙasar ta Aljeriya
Wannan shi ne babban abinda ke ɗaukar hankalin ƙasashen duniya da kuma masu yin sharhi akan al'amura. Louis Martiney wani masani ne, akan kimiyyar siyasa da ke a birnin Paris na Faransa a jami'ar Science Po. Ya ce zaɓin mutumin da zai gaje shi ba zai kawo wani sauyi ba akan harkokin siyasar ƙasar.
Ya ce: '' karɓar mulkin ba wani abu ne ba da zai janyo yan takara ba da yawa. matsayin shugaban ƙasa matsayi ne da sojojin ke ba da shi ga wanda suka so, abinda watakila zai ɗauki hankali jama'a shi ne zaɓen yan majalisun dokoki da na kananan hukumomi. Amma shi ma shin za a tsaya a yi shi cikin haske da addalci, ta yadda 'yan takarar masu zaman kan su ,za a dama da su ? Tun da an san cewar ofishin ministan cikin gida na Aljeriya shi ne ke shirya zaɓen.''
Wa sojoji za su naɗa a matsayin shugaba idan Bouteflika ya gaza ?
Tun lokacin da Aljeriya ta samu yanci gashin kai a shekarun 1962 kullum sojoji su ne ke zaɓar shugaban kasa su miƙa matsayin ga wanda suka amince da shi. To amma a wannan jikon ana kallon cewar wata kila ɓaraka tsakanin sojojin ta kuno kai.
Kuma manyan tambayoyin da ake jiran samin amsar su a gaba su ne cewar ko shugaba Abdelaziz Bouteflika ya na iya cewar ya kasa gudanar da mulki saboda rashin lafiyar, ya kira wani sabon zaɓe kafin karshen wa'adi. Ko kuma dai zai wakilta wani akan mulkin irin na Hugo Chavez, lokaci na gaba zai tabbatar mana da gaskiyyar lamarin.
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi