1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece kuce akan sakamakon zaɓen Laberiya

November 11, 2011

Ana fama da saɓani game da sakamakon zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar Laberiya dangane da ƙarancin masu kaɗa ƙuri'a da kuma barazanar 'yan adawa game da kai magana gaban kotu

https://p.dw.com/p/139OF
Shugabar Laberiya Ellen Johnson-SirleafHoto: dapd

►Shugabar ƙasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf ta samu gagarumar nasara a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa, sai dai kuma yawan waɗanda suka fita kaɗa ƙuri'unsu bai taka kara ya karya ba. Tun da farkon fari ne dai abokin takararta Winston Tubman yayi iƙirarin ƙaurace wa zaɓen, lamarin dake saka ayar tambaya a game da halascin shugabancinta. A yanzu bayan kammala zaɓen dai, babban abin da Johnson Sirleaf zata sa gaba shi ne haɗin kan ƙasar ta Laberiya da kuma shigar da 'yan hamayyar a sabuwar gwamnatin da za a naɗa.

Ɗaruruwan 'yan ƙasar Laberiya suka barbazu kan tituna suna ɗoki da murnar rahoton cewar Ellen Johnson-Sirleaf, mace mai kamar maza, zata sake jan akalar ƙasar har wasu shekaru shida masu zuwa.

A shekarunta na 73 da haifuwa, al'umar Laberiya sun ɗauketa tamkar uwa ce a garesu. To sai dai kuma ƙauracewa zaɓen da 'yan hamayya suka yi da kuma ƙarancin masu kaɗa ƙuri'a da aka samu ya kusa ya sanya murna ta koma ciki dangane da nasarar zaɓenta. Wani da ake kira Moses Marlee, dake ba wa Sirleaf goyan-baya ya bayyana takaicinsa game da zaɓen da ya kira wai na sharar fage. Domin kuwa ainihin gaggan abokan adawar shugabar da suka haɗa da Winston Tubman da mataimakinsa tsofon ɗan ƙwallon ƙafa George Weah sun ƙaurace wa zaɓen bisa zargin cewar an tafka maguɗi a zagayen farko. Amma fa dukkan masu sa ido na ƙasa da ƙasa sun yi fatali da wannan zargi. A jajibirin zagaye na biyu na zaɓen, magoya bayan Winston Tubman sun yi ƙoƙarin haɗa wani taro na kamfe kuma aka shiga tashin hankali. Dangane da haka da yawa daga al'umar Laberiyan suka shiga fargabar fita kaɗa ƙuri'a. Domin kuwa yawan waɗanda suka kaɗa ƙuri'un nasu bai kai kashi arba'in cikin ɗari ba. Amma duk da haka shugaba Sirleaf ta dage akan halacin shugabancinta:

"Wannan adadin na tabbatar da halascinmu kuma babban abin da zamu sa gaba na haɗa kan al'umar Laberiya zai ƙara tabbatar da wannan halasci."

Abdullai Kamara wani mai fafutukar tabbatar da demokraɗiyya ne a ƙasar Laberiya. Ya ce ko da yake ƙarancin masu kaɗa ƙuri'ar da kuma ƙaurace wa zaɓen na haddasa tababa, amma kuma ba zai yi wani tasiri akan ikon Sirlef na tafiyar da al'amuran mulki na.

Wahlen Liberia
Jami'an hukumar zaɓe na ƙididdigar ƙuri'un da aka kaɗaHoto: dapd

Sirleaf, wadda ta taba samun lambar yabo ta Nobel kuma ƙwararrar masaniya al'amuran tattalin arziƙi da aka yayeta daga jami'ar Havard ta Amirka, tana da gagarumin goyan baya daga kafofi na ƙetare. Sai dai duk da haka wajibi ne ta nemi hanyoyin da suka dace domin ɗinke ɓarakar dake addabar Laberiya. A wa'adin mulkinta da ya shige ta shigar da yawa daga tsaffin haulaƙan yaƙin Laberiya a gwamnatinta. A kuma wannan karon ta nuna sha'awar ba wa abokin takararta Winston Tubman mukami a gwamnati.

"Zan miƙa hannu ga dukkan 'yan takarar neman zama shugaban ƙasa, ko da yake ban san irin tayin da zan yi musu ba saboda ban fara mayar da hankali akan amanna da gwamnati ba."

Kawo yanzun dai Tubman ya ce ba zai amince da gwamnatin Sirleaf ba kuma zai ƙalubalanci sakamakon zaɓen a kotu. Sai dai abin da ake fargaba game da Laberiya shi ne ɓillar wani sabon tashin hankali duk kuwa da buƙatar zaman lafiyar da al'umar ƙasar ke yi bayan yaƙin basasar da ta sha fama da shi kwanan baya.

Mawallafi: Bennie Allen/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu