Cece-kuce kan nukiliyar Iran
September 18, 2014Amirka ta yi kira ga Iran da ta amince Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da wani bincike, wanda aka dade ana dagawa kan makamashi nukiliyarta, inda ta ce ya na da matukar mahimmanci ga yarjejeniyar da ita Iran ke tattaunawa da kasashen masu karfi na duniya, a wannan makon a birnin New York.
Laura Kennedy, wadda ke wakiltar Amirka a Hukumar kula da makamashi na duniya wato IAEA ta ce ta damu kwarai da irin jinkirin da ake samu wajen gudanar da wannan bincike, kuma akwai karin damuwar cewa mai yiwuwa akwai bangaren da ya shafi soji a makamashin nukiliyar na Iran, kuma dokle a biciki komai kafin a kai ga kulla wannan yarjejeniya.
Hukumar IAEA ta kan binciki ajiyar nukiliyar kasashe a kai-a kai, amma ta dade tana zargin cewa shirin nukiliyar Tehran ba na dalilan zaman lafiya ba ne kadai kammar yadda Iran ke jaddadawa a duk sadda batun ya taso