1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nadin dan adawa ya janyo suka a Kamaru

Zakari Sadou
April 5, 2023

Bai wa na kusa da shugaban jam'iyyar adawa ta SDF mukamin sanata da Shugaba Paul Biya yayi ya janyo cece-kuce tsakanin 'ya'yan jam'iyyasa.

https://p.dw.com/p/4PkUT
Paul Biya
Hoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

Karon farko kenan da shugaban Kamaru Paul Biya ya nada wani dan jam'iyyar SDF a wani matsayi a kasar. Jean Robert Wafo makusancin honorable Jean Michel Nintcheu mai ra'ayin rikau ya ce wannan na nuna alakar boye da ke tsakanin gwamnatin Paul Biya da SDF na Ni John Fru Ndi.

" Wannan abin bakin cike ne da ba a taba samun irinsa a tarihin SDF ba, dokar SDF ta ce, duk wata shawara da ya kamata a yanke mai muhimmanci tattare kuma da hatsari, dole ne a gabatar dashi a teburi domin tattaunawa kafin yanke hukunci ".

Da ba don wannan nadin ba,  da jam'iyyar mai alamar ma'auni bata samu kujera ko daya a majalisar ba, duba da zabukan uku da suka gabata bata samun kujeru. Wadanda aka zaba a shekarar 2018 wannan karon ba su taka wata muhimmiyar rawa a bana ba, amma dole su rayu a siyasance kamar yadda Alain Tongo ya ce:

" SDF ta yanke shawara kasancewa a dukkan cibiyoyin tafiyar da kasa musamman a majalisu kafin darewa kan damafun iko, majalisar dattabai waje na mahawara yana da kyau, abu ne mai muhimmanci kuma kamata yayi yan Kamaru sun rubanya wuraren zaman tattaunawa ".

A waje guda da akwai akidar jam'iyya wacce ita ce ginshikin tafiyarta idan ta rasa ta, tamkar ta rasa alkibla ga kuma dokokin jam'iyya wacce za ta iya bayyana dalilin nadin shugaban kasa. Dr Louison Essomba masanin harkokin shari'a ne a Kamaru:

"Wannan cin amana ce, da yake SDF bata amince ta shiga gwamnatin kawance ba har ta samu nadin daya daga cikinta, amma dole mu gane abu guda ita ce, dokar kasa ta baiwa shugaban kasa damar nada sanatoci 30, kenan wannan damar ta baiwa shugaban kasa damar magance rashin adalci da kuma gyara bacin rai dake nan tafe ".

Babban abin da ke nuna alamun buga gangar siyasa a Kamaru, shi ne tsayar da Joshua Osih da jam'iyyar adawar kasar SDF ta yi a matsayin dan takakar kujerar shugaban kasa a shekarar 2018 da ya sha kaye a hannun Paul Biya a ganinsu wannan kawai wata dama ce da SDF ta baiwa CPDM da ci gaba da mulki.

A 'yan kwanakin nan ne aka yi waje da wasu da aka yi wa lakabi da G27 wadanda ke adawa da siyasar shugaban na SDF ke yi kawo yanzu wanda a fadarsu yake taimakawa gwamnatin Yaoundé.

Shugaban Kamaru Paul Biya ya nada sanatoci 30 daga ciki ya baiwa jam'iyyun kawance kujeru 6 wadanda aka saba gani suna hulda da CPDM mai mulkin kasar tun tsawon shekaru 38 baya ga SDF sabuwar shiga.