Ana cigaba da kidayar kuri'u a Barkina Faso
November 24, 2020Talla
Ya yin da ake cigaba da kidayar kuri'u a zaben kasar da ya gudana a karshen mako, shugaba Roch Christian Kabore na kasar Barkina Faso ne ke kan gaba.
Dama can an yi hasashen cewa shugaban mai ci yanzu ne ake tsammanin zai lashe zaben da daruruwan 'yan kasar basu sami damar kada kuri'unsu ba, sakamakon abinda hukumar zaben kasar ta CENI ta ce matsalar tsaro ce ta haddasa hakan.
Shugaba Kabore da ke neman wa'adi na 2 ya fafata da 'yan takara 12, wadan da suka zargi tabka magudi a zaben. sai dai shugaban hukumar zaben kasar Newton Ahmed ya musunta wannan zargin.
An dai zargi gwamnatin kalkashin Kabore da gazawa wajen dakile hare-haren masu ikirarin jihadi a kasar.