1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ta ce ba za ta tura soji Nijar ba

August 5, 2023

Gwamnatin Chadi ta ce ba za tura sojojinta Nijar domin bai wa sojojin kungiyar ECOWAS gudunmawar dawo da dimukuradiyya ba.

https://p.dw.com/p/4Uo4I
Jagoran gwamnatin soji ta Chadi Mahamat Idriss Deby Itno
Jagoran gwamnatin soji ta Chadi Mahamat Idriss Deby ItnoHoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP

Gwamnatin Chadi kasar Chadi ta ce ba za ta shiga cikin ayarin kasashen da za su afka wa sojojin Nijar ba. Ministan tsaron kasar ne ya sanar wa 'yan kasar haka a ranar Juma'a daidai lokacin da sojojin kasashen Afirka ta Yamma suka ce sun kammala tsara yadda za su afka wa Nijar din madamar masu juyin mulkin suka gaza mayar da Shugaba Bazoum Mohamed kan karagar mulki.

Tun da farko dai makwabtan kasashe irinsu Mali da Burkina Faso da kuma Guinea sun yi gargadin duk wani mataki na amfani da karfi a kan sojojin Nijar, suna masu shan alwashin tallafa wa sojojin Nijar da suka hambarar da gwamnatin farar hula a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.

Sai dai a gefe guda, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya aike wa majalisar dokokin kasar a hukumance bukatar samun izinin jibge sojojin Najeriyar a Nijar idan har mahukunta soji na Nijar karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani suka gaza mika mulki a cikin wa'adin da kungiyar ECOWAS ta diba musu.