1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChadi

Chadi: Cin hanci da karbar rashawa na karuwa a mulkin Deby

Blaise Dariustone AH/MAB
September 11, 2024

'Yan adawa da 'yan farar hula sun yi tir da yaduwar cin hanci da rashawa a Chadi, biyo bayan fallasa daga jaridar Médiapart kan zargin 'yan kasahen waje da bayar da na goro don samun kwangilar gina wani otal a N'djamena.

https://p.dw.com/p/4kVVP
Shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby na fuskantar zargi kan cin hanci a Faransa
Shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby na fuskantar zargi kan cin hanci a FaransaHoto: Israel Matene/REUTERS

An gudanar da bincike a kasashen Beljiyam da Faransa inda aka yi wa wasu jami'an kamfanin gine-gine na CFE tambayoyi, saboda ana zargin su da karbar na goro a cikin wannan harkar ta gina katafaren otal a birnin Ndjamena na ksara Chadi. Lamarin ya faru ne kimanin shekaru goma da suka gabata, yayin da ake gina wani katafaren otel da ke karkashin kulawar Radisson Blu a babban birnin kasar Chadi. An kammala aikin gina wannan otal a shekarar 2017, amma har yanzu ba a biya kudaden da aka gina shi ba.

Karin bayani:Chadi: Zargin shugaban kasa da cin-hanci

Akwai kudade Euro miliyan 60 da ya kamata gwamnatin Chadi ta zuba wa kamfanin, amma ba ta zuba, kuma ana tsammanin gwamnatin ta ba da na toshiyar baki ga jami'an kamfanin ne ya sa aka yi musu wadannan tambayoyi. Wannan batu ne ya sa da yawa daga cikin 'yan siyasar kasar Chadi ke kauce wa yin mahawara a kan wannan matsala, 

 Al 'ummar kasar Chadi na da masaniya kan ta'adar cin hanci kuma suna yakar ta
Al 'ummar kasar Chadi na da masaniya kan ta'adar cin hanci kuma suna yakar taHoto: Blaise Daruistone/DW

Da yawa daga cikin al 'ummar kasar Chadi sun san wannan al'ada ta cin hanci, inda ko da kwangila ka nema, sai ka bayar da kashi 10% na kudin da za a biya kafin samun kwangila. Jacques Ngarassal da ke zama dan fafutuka ya ce baya ga Chadi, da yawa daga kasashen Afirka na tafiyar da wannan tsarin ci-mu-ci. Ya ce : " Wannan Al'amari na bayar da 10% kafin samun kwangila kafin samun damar gudanar da ayyuka, ya yi barazana da girgiza kasarmu tsawon shekaru da dama har ma a wasu kasashen na Afirka.''

A tsari na mulki na siyasa, an fi samun irin wannan tabargazar cin kare babu babbaka. Amma kwarraru na ganin cewar ko a kasashen da ake mulkin soji, shugabannin na saka ido, idan ba haka ba wasu masu muguwar aniya za su iya goga musu kaurin suna.

Karin bayanChadi: Kungiyoyin gwagwarmaya sun kafa Jam'iyyai: 

Foulah Baba Isaac, wanda shi ne shugaban kungiyar yaki da cin hanci da rashawa da almubazzaranci da dukiyya a Chadi, ya nuna rashin jin dadinsa kan rashin hukunta masu aikata laifukan cin hanci da rashawa. Ya ce: "An sha ambato kasar Chadi a cikin batun cin hanci da karbar rashawa. Ko da a kididdigar da kungiyar Transparency International ta fitar, kasar Chadi ba ta a matsayi mai kyau, kasa ce da ke fama da cin hanci da rashawa, kuma kowa na iya wawurar dukiya a kasar Chadi ba tare da an hukunta shi ba, matikar yana da alaka da siyasar da ke yin mulki."

Madugun adawan Chadi Succes Masra na yin tir da cin hanci da karbar rashawa
Madugun adawan Chadi Succes Masra na yin tir da cin hanci da karbar rashawaHoto: Issouf Sanogo/AFP

Max Kemkoye, shugaban jam'iyyar Union Democrat ta Chadin ya ce iko ba ya tsawatawa. Ya ce " Rashin cibiyoyi masu karfi ne ya sa wannan tabarbarewar kudi ta ci gaba tun daga gwamnati har zuwa sauran ma'aikata, an dade ana yi almudahanar kudin ruwa da cin hanci na tsawon shekaru 30, har ya durkusar da kasarmnu."

Karin bayani:Chadi: Succes Masra zai yi takara

Tun lokacin da shugaban Chadi Mahmat deby ya dare kan karagar mulki, ya sha alwashi matsa kaimi wajren yaki da satar dukiyyar kasar da kuma yaki da cin hanci. Amma shi kansa akwai zarge-zarge da ake yi masa a Faransa na fuskantar shari'a a kan cin hanci.