Chadi: Mutuwar Habre ta bar baya a kura
September 2, 2021A baya bayan dai wasu jam'iyyun siyasar Chadi sun gindaya sharadin yi wa Hissène Habré afuwa gabanin su halarci taron tattauna al'amuran kasar da ake shirin yi a karshen wannan shekara. Jacqueline Moudeina wata 'yar fafutika kuma lauyar hadin gwiwar wadanda aka ci wa zarafi a yayin mulkin danniyar tsohon shugaban kasar na Chadi Hissène Habré ta ce Hissène Habré ya karya dokokin kasa. A fusace Jacqueline Moudeina ta bayyana wannan yunkurin na wasu jam'iyyuns siyasar Chadin a matsayin cin fuska tana mai cewa ko kadan ba za ta yi wannan fatan ba duba da yadda aka ci zarafin bil' Adama a baya. Ta ce: ''Mun yi nasara a shari'ar Hissène Habre domin har an yanke masa hukumci, amma kuma har yanzu ba mu yi nasarar biyan wadanda gwamnatinsa ta ci wa zarafi ba. Mutane ba sa son zaman tattauna kan teburi guda da sauran 'yan kasa sai su dinga neman wata kafa kawai. Wannan batun ko gobe ba za a taba manta da shi ba." Da dama dai a kasar ta Chadi masu ra'ayi irin na Jacquline na yi wa tsohon shugaban mulkin danniyar kasar ta Chadi Hissène Habré kallon wani shu'umin mutun. A karshen wannan shekarar ne dai ake sa ran gudanar da babban taron kasar Chadin mai shirin tattauna al'amurran siyasar kasar da suka sukurkuce, tun bayan rasuwar tsohon shuagban kasar Idriss Deby Itno.