Chadi: Wadanda aka azabtar sun koka da rashin diyya
November 10, 2017Alkalan da ke kare wadan da suka dandana kudar su a zamanin Hibre, sun kai karar gwamnatin Chadi a kungiyar hadin kan Afirka. A baya dai kotu ta umarci gwamnati da ta biya kudi dalar Amirka miliyon 125, a matsayin kudin diyya bayan samun jami'an tsaro 20 n a mulkin tsohon shugaban Chadi da laifukan da suka hada da kisan kiyashi da aikata fyade da cin zarafi ta hanyar musgunawa, laifukan da kotun ta ce ya keta haddin dan adam.
'Yan kasar Chadi dubu 7,000 da abin ya shafa sun koka kan yunkurin gwamnatin kasar na neman danne kudaden diyar su da kotu ta ba da umarni a biya shekaru biyu da suka gabata. A yanzu dai a tun watan Afirilu, wata kotun daukaka kara da ke Senegal ta tabbatar da hukunci daurin rai da rai kan tsohon shugaban kasar ta Chadi, Hissene Habre.